YADDA SHUGABANNIN NIGERIA SUKA SACE ARZIKIN KASA

by Datti

 

Shugaban ‘yan gwagwarmaya babban Kwamandan askarawan Salafiyyah a Nigeria shahidi Insha Allah Marigayi Sheikh Muhammad Auwal Adam Albaniy Zaria yace:

Ku je ku buga (www . globalforum . com) zaku ga tsohon shugaban hukumar EFCC Nuhu Ribado yake cewa, daga shekarar 1960 zuwa 2005 shugabannin Nigeria sun sace dala biliyan dubu dari biyar ($500,000,000,000)

Da masu kididdiga suka fitar sai sukace duk dan Nigeria a karkashin wannan kudin da aka sace mun kai mutum miliyan dari da hamsin, za’a iya bawa duk wani ‘dan Nigeria kudi Naira Miliyan goma, kuma kudin ya ragu

Ance har wanda aka haifa ana cikin lissafi tun ba’a san sunanshi ba shima zai samu miliyan goma, kuma kudin zasu ragu daga cikin wadanda aka sace, banda kudaden da ake dasu a kasa, kai idan ka kalli abinda akayi akan kudin wutar NEPA kawai ya isheka ka gane mawuyacin halin da ake ciki a Nigeria

Sannan kaje ka sake buga www.saharatv.com/obasanjo ko kuma ka tafi kan www.youtube.com sai ka tafi search bar ka rubuta Obasanjo, zaka ga scandal da massacre da suka faru a zamanin mulkin Obasanjo, anan zakaji yaran Obasanjo ne gasu nan yarbawa sukace saboda scandal din NEPA Obasanjo ya sa aka kashe Bola Ige, yasa aka kashe wane da wane, video ne ba ma text ba a Internet, ‘ya’yan yarbawa ne suke magana akan Maigidansu Obasanjo

To jama’a wannan shine halin da muke ciki a Kasar, amma duk da haka ka ga mun rayu, har muna magana, mun karya, kuma mai yiwuwa zuwa anjima ma zamu sake cin abinci, to mu godewa Allah, kuma mu cigaba da yin addu’ah Nigeria zata gyaru, amma zata gyaru kayi kokari ka zama daya daga cikin wadanda Allah zaiyi aiki da su wajen gyara Kasar

Amma fa wannan baya nuna kaima zakayi zalunci, kaima sai ka hakura da zalunci, don ba za’ayi ja ya fado ja ya dauka ba, shine abinda ayake faruwa a irin Kasashen Congo, Liberia da Sierra Leone, an kori wane azzalumi ne, wane kuma ya zo ya fishi zalunci

Tambaya itace ina kudaden da aka karbo a hannun ‘ya’ya da zuriyar Abatcha? shine ja ya fado ja ya dauka, ance wane ya sata, bayan an karbo kuma sai ace wane eh to shikenan dauki kaza dauki kaza, to shi can ya sata ba’a sani ba, kai kuma sai da aka sani tukunna ka sata

Allah Ka karbi shahadar Malam Albaniy Zaria

You may also like

Leave a Comment

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More