NURU KHALID DAN INTERFAITH NE

by Datti

NURA KHALID DAN INTER-FAITH NE BA AHLUSSUNNAH BA

Ya kamata Malaman Ahlussunnah su fito su fadawa Musulmin Nigeria gaskiya akan akidar Nuru Khalid Nyanya Abuja da makamantansa

Marigayi Malam Albaniy Zaria tun yana raye ya tona asirin akidar Nuru Khalid wanda yake asalinsa dan Izalar Jos ne, kuma surukin daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar Izala Marigayi Sheikh Ibrahim Bawa Maishinkafa, amma daga baya ya fita daga Izalar

Sheikh Nuru Khalid ba Ahlussunnah bane, ba Salafiyyah ba kuma ba Izala ba, asalima yana fada da wadannan akidu , akidar da yake kanta a yanzu itace akidar Inter-Faith

Macece Akidar Inter-Faith?
Inter-Faith mummunan akidace na turawan yammacin duniya karkashin tsarin su na New World Order wanda suke da buri na kafa sabuwar duniya wacce babu addini a cikinta

Inter-Faith yana nufin kulla alaka da daidaita tsakanin addinai a matsayin abu daya, Musulmi ya dena kiran wanda ba Musulmi ba a matsayin kafuri ko da ayoyin Qur’ani sun kirasu kafurai, Musulmai su dena da’awar kiran wadanda ba Musulmai ba cikin addinin Musulunci, wai a bar kowa ya tsaya akan addininsa sai anje lahira za’a san wanda yake kan gaskiya, a hada kai a zama abu daya, wai da hakane za’a samu zaman lafiya

A cikin akidar Inter-Faith akwai imanin cewa wanda ba Musulmi ba ma zai iya shiga Aljannah, azo a hada kai da kowa, a kawar da zazzafan kishin addini, hatta ‘yan Luwadi da ‘yan Madigo da masu auren dabbobi za’a hada kai da su a cikin akidar Interfaith, sannan za’a dena sukar su, kuma karshe abinda “Interfaith” ke kai mutum shine “Atheist” wato akidar babu Allah abin bauta

Kamar yadda Malam Albaniy Zaria ya bayyana, yace akidar Interfaith kwangila ce kai tsaye daga Amerika, kuma Bill Gate babban jigo ne a cikin yada akidar ta Interfaith, ba Nurul Khalid ba, akwai manyan Malamai da Malam Albaniy ya zayyano sunayensu wanda suke akan akidar Interfaith, kuma makudan kudi ake biyansu

Inter-Faith mummunan akidace turawa suka kawo suka damka a hannun gurbatattun Musulmai domin a raunata Musulunci a kuma yaki kyakkawan akida na Musulunci, wanda idan aka bar akidar Interfaith ta cigaba da yaduwa to ba shakka an dauko hanyar ruguza Musulunci

Jama’a ku ziyarci shafin facebook na Nuru Khalid, yanzu ya bayyana kansa karara akidar Interfaith yake yadawa, har ma ya rubuta Littafi a kai, sannan yayi khudubar juma’a akan akidarsu na Interfaith

Don haka ‘yan jaridun bogi da suke alakanta Nuru Khalid da Ahlussunnah ko izala ko Salafiyyah ba burgeshi kukeyi ba, domin bayaso a alakantashi da wannan, akidarsa kenan Interfaith

Muna fatan Allah Ya shiryar da su, idan ba zasu shiryu ba Allah Ya amintar da Musulmai da Musulunci daga akidarsu na Interfaith Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum

You may also like

Leave a Comment

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More