SUN FI MUSULMAI AIKATA TA’ADDANCI

by Datti

MUSULUNCI BA ADDININ TA’ADDANCI BANE

(1) Wadanda suka tayar da yakin duniya na farko ba Musulmai bane

(2) Wadanda suka tayar da yakin duniya na biyu ba Musulmai bane

(3) Kungiyar ‘Yan ta’adda na farko a tarihin duniya Ku Klux Klan (KKK) ba Musulmai bane

(4) ‘Yan darikar Protestant na farko da suka fara tawaye wa Malaman addinin nasara suka dinga kashe malaman a Kasar Ingila ba Musulmai bane

(5) Wanda ya kashe yahudawa sama da Miliyon 6 a Kasar Jamus ba musulmi bane

(6) Wadanda suka jefa makamin kare dangi (Atomic bomb) a yankin Hiroshima da Nagasaki na Kasar Japan ba Musulmai bane

(7) Wadanda suka kashe Indiyawa sama da mutun miliyon 100 a Arewacin Amurka ba Musulmai bane

(8) Wadanda suka hallaka Indiyawa sama da mutum miliyan 50 a kudancin Amurka ba Musulmai bane

(9) Wadanda suka bautar da mutanen Afirka sama da mutum miliyon 180 a matsayin bayi kashi 88 cikin 100 aka kashe su aka jefa gawarwakinsu a kogin Atlantic ba Musulmai bane

(10) Yahudu da Nasara sunfi kowa sanin cewa Musulmai ba ‘yan ta’adda bane, abinda yake faruwa na ta’addanci yau a duniyar Musulunci su ke tsarawa da kuma haddasawa don su bata Musulunci

(11) Wadanda sukayi kisan kabilanci na mutane sama da Miliyon 20 a Kasar Australia ba Musulmai bane

(12) Wadanda suke yiwa Palasdinawa kisan gilla suna rushe gidajensu suna mamayar Kasarsu ba Musulmai bane

(13) Wadanda suke yiwa Musulmi ‘yan kabilar Rohingya a Kasar Myanmar kisan gilla ba Musulmai bane

(14) Ga tarihi mutum daya Adolf Hitler cikin wadanda ba Musulmai ba ya aikata ta’addancin da tunda Allah Ya halicci duniya taron jama’ar Musulmin gaba dayansu basu aikata ba

(15) Abinda suke nufi da ta’addanci shine duk wanda ba Musulmi idan ya aikata laifi sunansa laifi, idan Musulmi ne ya aikata sunansa ta’addanci don su samu hujjar da zasu yakeshi

(16) Musulunci ba addinin ta’addanci bane, kungiyoyin da suke amsa sunan Musulunci a yau suke ta’addanci aikin sirri ne na hukumar leken asiri da tattara bayanan sirrin tsaron duniya na Kasar Amurka (American Central Intelligence Agency CIA Covert Operation)

Yaa Allah Ka kare Musulunci daga sharrin yahudawa Amin

You may also like

Leave a Comment

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More