HATSARIN DA MATA SUKE FUSKANTA

by Datti

MATAN DA SUKE SAKA HOTON SU A MEDIA ABIN TAUSAYI NE

Datti Assalafiy✍️

Wani bincike da na gabatar akan matan da suke yada hoton su a facebook yasa na gano cewa sun fi kowa fuskantar hatsarin lalacewa fiye da kowa a duniyar facebook da sauran kafofin sada zumunta

Wato a duk lokacin da mace ta saki hotonta a facebook, musamman idan ta shafa hodar a cuci maza tayi haske tana kyalli, ko tayi amfani da wani application ta gyara hoton tayi posting dashi, sakonnin maza musamman fasikai sai sun cika inbox dinta, kuma mafi yawan masu tura sakon ta inbox lalatattu ne

Wata a haka zata hadu da wani ‘dan iska ya yaudareta da ‘yan kudade kadan yaje ya lalata mata rayuwa, na rantse da girman Allah babu wata mace da take yada hotonta a dandalin sada zumunta da zata tsallake wannan hatsari na lalacewa sai kalilan daga cikinsu

Clue da zan baku jama’a shine, ku bude facebook account da sunan mace, sannan ku nemi hoton wata mace mai haske ku saka a profile, sannan ku dinga yin posting da hoton mace a shafin, zaku fahimci bincike na gaskiya ne

Duk wata macen kirki da ta san ciwon kanta zatayi kokari wajen gujewa yada hotunanta a kafofin sada zumunta, sai dai ga wacce bata san hatsarin da take kokarin jefa kanta ba kafin ranar da zatayi nadama marar amfani ya sameta

Shiyasa nake cewa, duk macen da take sakin hotonta a dandalin sada zumunta tanayi saboda dalili guda daya cikin dalilai uku ne:
1-Tana neman mijin aure
2-Tana tallata kanta ga mazinata
3-Saboda ta jahilci hatsarin saka hoto a media

Nafi tausayin wacce take saka hotonta a media saboda ta jahilci hatsarin abin, sannan sai wacce take neman mijin aure a dalilin yada hotonta, wadannan abin tausayi ne, amma wacce take yada hoto saboda neman mazinata wannan ba abar tausayi bace

‘Yar uwa idan kina saka hoto a media saboda jahilci ne to ki dena, domin yana tattare da hatsari babba, idan kina sakawa saboda neman mijin aure ne, to hakika zaiyi wahala ki dace da mutumin kirki, domin duk wani mutumin kirki baya son macen da take yawan mu’amala da maza da yawa har idonta ya bude, balle wacce take yada hotonta a media inda mutane ba adadi zasu gani su tura sakon sirri

Mata masu saka hoton su a media basa jimawa a gidan aure auren ya mutu saboda illar saka hoto a media, sannan ki sani duk abinda kika saka a kafar yanar gizo zai tabbata har abada, yaranki da jikokinki zasu zo su gani idan kin auru kenan baki tsufa a gaban iyayenki ba kafin “menopause age”

A kafofin sada zumunta akwai mutanen banza wanda suke tallata hajojinsu na iskanci da masu neman jinsi suna daukan hotunan matan da suka gani a media, sai su bude account na iskanci su saka hoton a profile, akan haka ansha samun matsala da matan da aka dauki hotonsu a media

Wani dan iskan kuma haka kawai zai dauki hoton gabansa ko wani hoton tsiraici ya tura ta inbox din wata mace, duk don ya yaudareta kawai, hanyoyi da yawa gashi nan ‘yan iska na amfani dashi wajen kokarin sai sun lalata tarbiyyan matan media

Mun bi diddigin wani yaro wanda ya bude group WhatsApp yana hada mazinata a ciki, baya saka mutum a cikin group din sai wanda ya biya kudi, sai yayi amfani da sunan mace, ya dauki hoton matar aure a facebook ya saka a profile na group din, anyi shari’a sosai, matar da kyar ta sha da aurenta

Na taba ganin matar da akayi posting da hoton ta a facebook akace tana neman wanda zai kwanta da ita, alhali karya aka mata, me ya jawo haka? saboda tana sakin hotonta a media, idan kika bincika kika nutsu kika auna zaki ga cewa rashin saka hotonki a media yafi zama alheri sosai fiye da saka hoton, sai dai idan kinayi saboda daya daga cikin dalilai guda uku da na bayyana a sama, musamman neman mijin aure da kuma neman abokin lalata

Kuma magana ta gaskiya mafi yawan matan da suke sakin hotonsu a media ba kyau suke dashi ba, hasken powder na acuci maza ne da kuma application, duk wani abu mai kyau boye shi ake, hakanan duk wani abu mai daraja boye shi ake, ki sani cewa mutanen kirki sun san da wannan, duk mutumin kirki da ya ga hotunanki a media ya san cewa bugun china ne ba tabbas

Allah Ya sa ku fahimta, ku gyara

You may also like

Leave a Comment

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More