ANCI AMANAR TSARON NIGERIA?

by Datti

RUBUTAWA: Datti Assalafiy

HIRAN ZUCI…

Misali nake bayarwa a cikin zuciyata

Inda ace ni Datti Assalafiy nine shugaba Muhammadu Buhari tsohon General a gidan Soji wanda nake da wayewa akan dabarun yaki, tsaro da tsageranci, zan kira taron sirri da masu iko da tsaron Nigeria gaba dayansu a wani kebantaccen guri na sirri, kafin su shiga dakin da zamu gudanar da taron zan rabasu da wayoyin dake jikinsu, zan rabasu da duk wata na’urar sirri da take nadar bayanai a boye, zan kafe na’ura da zata nadi bidiyo da audio na tattaunawar sirri da zanyi da su

Zan fada musu cewa a gurguje sannunku da zuwa, ba zaman shan shayi da cool drinks ya sa na kira wannan zaman sirri ba, ku sani cewa Nigeria ta kama da wuta, talakawa sunzo wuya, ina ji mana tsoron tawaye da juyin juya hali, munzo madafun ikon Nigeria saboda jama’ar Nigeria da suka zabemu, duk abinda muka samu ta dalilinsu ne

Kafin zabe, munyi kanfe da matsalar tsaro, duk inda mukaje yawon zabe muna fada wa jama’a cewa PDP ta lalata Nigeria, PDP taci amanar ‘yan Nigeria ta damkawa Boko Haram garuruwa masu yawa a Arewa maso gabas, lamarin tsaro ya tabarbare a mulkin PDP, muka yiwa ‘yan Nigeria alkawarin cewa zamu gama da matsalolin tsaro a watanni 6 na farkon mulkin mu, yau muna shekaru 6 a mulki mun gagara cika wannan alkawarin, ina ji a raina kamar na ajiye mukamina na shugaban kasa saboda takaici

Da haka muka gamsar da talakawan Nigeria suka zabemu, da na zama shugaban kasa na zabo ku na baku wadannan manyan mukamai na tsaro domin ku taimakeni mu cika alkawarin da muka yiwa jama’ar Nigeria, ina ji a raina kamar na saka kakin soji na shiga jeji da kaina yakar ‘yan ta’adda, amma tsufa ya kamani, imbanda haka da nayi irin yadda Gwarzon Afirka Field Marshall of Chad Marigayi Idris Deby Itno yayi, da na yi irin yadda sabon Prime Minister na Kasar Ethiopia Aby Ahmad yayi inda ya saka kakin soji ya tafi fagen daya ya jagoranci sojojin kasar fafatawa da ‘yan tawayen Tigray

Magana ta gaskiya babu boye-boye tsakani na daku domin ta bayyana gaskiya cewa mun gaza a fannin tsaro, security is our number one priority amma mun gaza, musamman a bangaren yaki da masu garkuwa da mutane wanda bayanan sirrin tsaro suka tabbatar cewa sun hada kai da ‘yan Boko Haram da Ansaru

Talakawa suna kuka masu garkuwa da mutane sun addabesu, hanyar Kaduna zuwa Abuja ta zama tarkon mutuwa, garuruwa masu yawa a jihohin Arewa maso yamma suna hannun ‘yan bindiga suna karban haraji sai kace Gwamnati biyu ake dashi a Kasar saboda tabarbarewa, wannan babban abin kunya ne garemu, mu shugabanni bama tafiya a cikin mota sai jirgi watakila shiyasa bamu fahimci halin da talakawa ke ciki ba, sannan duk inda zamu je akwai rakiyar jami’an tsaro a tare damu, wannan rashin adalci ne

Ku dubi yadda mukayi amfani da International Intelligence muka kama shugaban kungiyar IPOB Nnamdi Kanu a Kasar Kenya bayan ya baro inda yake a Ingila yazo Asibiti a Kenya aka masa aiki a zuciyarsa, mun kamashi har yayi kwana uku a hannun mu hatta Amerika da Ingila basu sani mun kamashi ba, munyi amfani da dabaru na ilmin tsaro muka kama wanda yake yiwa siyasar mu babban barazana, ina kuwa wadanda basu kai Nnamdi Kanu hatsari da karfi da goyon baya ba ace sun gagaremu ba? ba zan yadda da wannan rainin wayo da rainin hankali ba!, shin ko don Nnamdi Kanu yana yiwa siyasarmu barazana ne muka bada muhimmanci wajen dakileshi su kuma masu garkuwa da mutane suna yiwa talakawa barazana ne?

Muna da isassun kayan aiki na zamani, muna da manyan motocin yaki masu sulke, muna da sabbin jiragen yaki na zamani, muna da kwararrun jami’an tsaro masu jini a jika, muna da jirage masu leken asiri, muna da taswira na duk wata maboya na ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a fadin tarayyar Nigeria, muna da ingantattun kayan aiki na zamani da ake leken asiri da su, muna da iko da karfin da zamu iya shiga kowani irin lungu da sako a Nigeria mu kawar da duk wani dan bindiga ko dan ta’adda

To ya kamata mu sani cewa watanni 18 ya rage mana a mulkin Nigeria, zamu koma cikin talakawan nan mu karasa rayuwa da su, ya zama wajibi a garemu muyi abinda ya dace wajen gamawa da wadannan jahilan ‘yan bindiga kafin iko da Abuja ya kubuce daga hannu mu

A matsayina na shugaban kasar Nigeria, zan baku wa’adin wata 2, duk wani shugaban ‘yan bindiga ina so a kawoshi Abuja a raye ko a mace, idan wata 2 ya cika bakuyi abinda na umarta ba, to kafin ku dawo gareni ku tabbata kun cire kakinku na aiki, masu bani shawara akan tsaro da manyan daraktoci na tsaro ku tabbata kun rubuta takardan ajiye aiki, zan kawo wadanda zasu iya

Daga nan ba zan saurari karin jawabi daga bakin kowa ba, zan tashi nayi tafiyata, ba zan sake karban kiran wayar wani daga cikinsu ba, ba zan sake aminta da rahotannin su na tsaro ba imba nasara na gani a zahiri ba, ba zan sake tafiya kasar waje ba, zan bibiyi dukkan abinda zai gudana ta wata hanyar sirri, idan naga alamu wata biyu zasu cika basuyi abinda ya dace ba zan musu ritaya na koresu na kawo sabbin jini matasa da zasu iya tun kafin wa’adin da na basu ya cika

A matsayina na Datti Assalafiy wanda nake karatun jami’a a bangaren kimiyyar laifuka da karatun tsaro ni kadai nake wannan hiran a cikin zuciyata

Muna rokon Allah Ya amintar damu daga dukkan sharri

Arewa Intelligence
25-11-2021

You may also like

Leave a Comment

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More