ABINDA BAKU SANI BA GAME DA MASALLACIN HARAMI

by Datti

Rubutawa: B Salia Sicey

A yayin da ka yi arangama da Ka’aba girmanta zai na ka mamaki don ta wuce duk yadda ka ke tunani

Masallacin Harami da ke Birnin Makka na kasar Saudiyya shi ne masallaci mafi girma da tsarki a ban-kasa.

Shi ne masallacin da ake nunka ladan sallah sau dubu dari fiye da sallah a sauran masallatai.

Masallacin Harami ne na farko daga cikin masallatai uku mafi daraja a duniya, da suka hada da Masallacin Annabi SAW da ke Madina, da kuma Masallacin Kudus da ke Isra’ila.

A cikinsa ne Dakin Ka’aba yake, wanda shi ne ginin farko a duniya kamar yadda musulunci ya nuna, kuma shi ne Al-Kiblar da Musulmai ke kallo a duk lokacin da za su yi sallah daga ko ina a duniya.

A can ne ake cika wasu sharudan daya daga cikin shika-shikan musulunci biyar da ake so kownne musulmi ya sauke idan ya samu iko, wato aikin Hajji, kamar Dawafi da Sa’ayi tsakanin Safa da Marwa.

Ga wanda bai taba zuwa wannan waje ba zai so ya san yaya wajen yake.

Girman Masallacin

Girman Masallacin Harami na Makka ya kai murabba’in mita 356,800, kuma yana iya daukar kusan mutum 800,000 masu ibada a lokacin aikin hajji, kamar yadda shafin intanet mai kula da masallacin ya ruwaito.

An kawata wannan masallacin da hasken wutar lantarki tarwal ta ko ina, ta yadda da wuya mutum ya gane lokacin faduwar rana.

Akwai lifta da dama da ke kai mutane sama da saukar da su kasa, da matakalar bene mai tafiya da kanta.

Akwai ginin karkashin kasa. An shimfide dadumai ta ko ina a cikin masallacin in ban da harabar Ka’aba, an kuma girke manyan kuloli shake da ruwan zam-zam domin mutane su sha.

Bandaki

An gina bandakuna na zamani ta kowacce kusurwar masallacin domin miliyoyin mutanen da ke zuwa su samu damar zagayawa ba tare da samun cikas ba.

Kazalika an kuma ware na mata daban, na maza daban. Dukkan kayyakin amfanin na zamani ne, kuma masu aikin tsaftace wajen suna nan ba dare ba rana, inda suke tsaftace su.

An kuma sanya alamar da ke nuna bandakin maza daban na mata daban, inda aka kafa allon sanarwa da Larabci da kuma Turanci.

Manyan abubuwan da ke cikin masallacin

A wannan tsarkakakken masallaci akwai Ka’abatul Musharrafa, wato Dakin Allah Mai Tsarki, inda nan ce alkiblar da duk musulman duniya ke fuskanta idan suna salla.

Tsawon Ka’aba ya kai mita 12, fadinta kuma mita 10 sannan tudunta ya kai mita 15.

An lullube ta da Bakin Yadi da ake kira Kiswah, wanda yake dauke da rubutun Kur’ani mai girma da ruwan gwal. Duk shekara ake sauya Kiswah.

Kofar shiga Dakin Ka’aba tana daga bangon arewa maso gabashin dakin.

A jikin Ka’aba akwai Bakin Dutse, wato Hajrul Aswad inda daga nan ne ake fara dawafi, kuma ana so mai dawafi ya sumbanci dutsen, in ya samu dama.

In kuma bai samu damar sunbata ba, sai ya taba da hannu, ko kuma ma ya nuna shi da hannu in bai samu damar tabawar ba.

Multazam ma wani bangare ne na Ka’aba da masu ibadah kan tsaya don yin addu’a. Yana tsakanin dutsen Hajarun Aswada da kofar Ka’aba.

Ana so idan mutum ya samu dama ya kara kirjinsa da cikinsa da hannayensa a wajen. Yana daga wuraren amsa addu’a. Fadinsa ya kai mita biyu.

Akwai kuma Makamu Ibrahim inda a bayansa ne ake so a yi sallah raka’a biyu bayan kammala dawafi. A nan ne aka ajiye dutsen da ke dauke da alamar sawun Annabi Ibrahim AS wanda ya taka lokacin da ya ke ginin Ka’aba.

Hijri Isma’il wanda ake kuma kira Hateem wani bango ne a jikin Ka’aba. An zagaye bangaren kadan, kuma yana daga bangaren arewa maso yammacin Ka’aba. Wajen shi ma yana cikin Ka’abah.

Kuraishawa ne suka fitar da shi daga Ka’aba lokacin da suka sake ginin dakin. Sun kasa shigar da shi cikin dakin ne saboda rashin kudi.

Sun shardanta cewa da kudin Halal kawai za a iya amfani wajen ginin, abinda ya janyo ke nan suka rage girman dakin saboda gaza samun isasshen kudin halal domin aikin.

Dutsen Safa da Marwa kamar yadda Allah ya fada a Alkur’ani mai girma “Lallai ne Safa da Marwa suna daga wuraren ibadar Allah, to, wanda ya yi aikin Hajji a dakin ko kuwa ya yi Umra, to, babu laifi a kansa ya yi dawafi tsakaninsu. Kuma wanda ya kara yin wani aikin alheri to, lallai ne wadannan su ne shiryayyu.” Surah Bakara aya ta 158.

Dutsen Safa inda daga nan ake fara Sa’ayi yana da nisan kilomita 0.80 daga Dakin Ka’aba. Yayin da Dutsen Marwah yake da nisan mita 100 daga Dakin Ka’abah.

Nisan da ke tsakanin duwatsun biyu kuwa mita 450 ne.

Rijiyar Zam-zam

Rijiyar Zam-zam na daga bangaren gabas da Ka’aba da nisan mita 20.

Wannan rijiya na samar da isasshhn ruwan da bai taba kafewa ba tun lokacin da Ubangiji Subhanahu Wa Ta’ala ya samar da ita a zamanin Annabi Ibrahim AS, kamar yadda malaman tarihi suka ruwaito.

Kofofin masallacin

Akwai kofoi biyar wadanda su ne manya-manya a Masallacin Harami da suke hada da:

Kofar Sarki Abdulaziz – Bab Abdulaziz

Kofar Fateh – Bab Fateh

Kofar Safa – Bab Safa

Kofar Umra – Bab Umra

Kofar Sarki Fahad – Bab Fahad

Sai kuma wasu kofofin kamar:

Baab Ibrahim

Bab Wedaa

Bab Ali

Bab Abbas

Babun Nabi

Bab Salaam

Bab Ziyarat

Bab Haram

Akwai kuma kananan kofofi bayan wadannan, inda idan aka hada su sun zama kofofi 95.

Kubbobi

Akwai manyan Kubbobi guda hudu da aka gina su a kan kofofin Bab Fatha da Bab Abdulaziz da Bab Umra da Bab Safa.

Sai kuma kananan Kubbobi 48. Jumullar kubbobin sun kama 52 kenan.

Akwai matakalar bene masu amfani da inji guda 56 a baki dayan masallacin, da ake kira Escalator da Turanci.

Akwai Hasumaya guda tara a Bab Fahad da Bab Abdulaziz da Bab Umra da biyu a Bab Fath da Bab Safa.

Tsawon hasumayoyin sun kai mita 92.

Limamai

Manyan limaman masallacin goma ne

Manyan limaman masallacin su ne:

Abdul Rahman Al-Sudais

Saud Al-Shuraim

Abdullah Awad Al Juhany

Saleh Al Talib

Saleh Al Humaid

Bandar Baleelah

Usaamah Khayyat

Yaseer Al Dosari

Khalid Al Ghmadi

Maher Al Muaiqly

Yadda ake wanke masallacin harami da kewaye

A na wanke dakin Ka’abah sau biyu duk shekara. Ana wanketa ne da ruwan da aka cudanya da turaren oud, da ruwa mai kanshin furrai, da kuma ruwan zam-zam.

Manyan shugabannin Saudiyya ne ke jagorantar wankin, tare da wasu shugabannin musulmai na duniya da ake gayyata.

Ana nuna wata irin kwarewa da bajinta wajen wanke filin masallacin, wato wajen da ake dawafi a kasa da minti 30.

Haka kuma ana wanke duka tayil din da ke cikin masallacin da kewaye, da kubbobi, da hasumiyoyi, da durkoki, da gadoji da kuma kofofin masallacin a kullum.

Akwai matakalar bene mai amfani da lantarki da dama a harabar masallacin

Su ma magudanan ruwan da ke masallacin ana wanke su da sabulu da maganin kwari.

Wuraren da ake wankewa sun hada da wajen Safa da Marwa, da ma harabar masallacin daga waje

Dubban ma’aikata ne ke hidimar tsaftace masallacin

Fadin wajen da ake wankewa a kullum ya kai murabba’in mita 700,000. Sannan idan an kammala aikin fadada masallacin, girman wajen da ake wankewa zai kai murabba’in mita miliyan daya da dubu dari takwas.

Shinfidun darduman alfarma da ke masallacin sun kai 30,000, kuma a ko da yaushe suna kasancewar tsaf-tsaf gami da kanshi. An kafa wani wajen wanken darduman na zamani na musamman domin wanke shinfidun masallacin kawai.

Sau uku ake wanke shinfidun a kullum. Sannan ana bin matakai har zuwa biyar wajen wankewar. Matakan suna farawa ne da kade musu kura, da wanke su, da matse su, da shanya su a rana, sannan a nannade su.

Su kuwa wuraren alwala da na shan ruwan zam-zam ana wanke su ne sau biyar a kullum. Su kuma bandakai (mekawayi, bayan gida) da yawansu ya kai 14,000 ana wanke su sau hudu a kowace rana.

Duk da dubban mutane da ke shiga wuraren na ibada, ana wanke wuraren ba tare da an shiga rayuwar masu ibada ba.

Sama da mutum 200 ke sa ido domin ganin an tsaftace wuraren ibadar yadda ya kamata.

Mutum 27,000 ne ke aikin wanke wuraren na ibada, yayin da mutum 100 ke sa ido wajen ganin an yi tsaftace wuraren yadda ya kamata.

Akwai kuma motoci 40, da motocin daukar shara 120, da motoci 60 na musamman masu wanke wuraren ibadar da ake amfani da su yau da gobe.

Yawan sharar da ake kwashewa da kullum ta kai tan 25, amma a lokacin da aikin Hajji da Umara da ake samun karuwar jama’a, yawan sharar yana kai wa tan 90.

Otal-Otal

Akwai manya-manya otal-otal da baki mahajjata ko masu Umra ke sauka wadanda ke daf da wannan masallaci.

A cikinsu akwai Darul Tauhid da Zam-Zam Towers da Makkah Hilton da Makkah Millenium da Swissotel Almakam da dai sauran su.

Masarautar Saudiyya tana ware miliyoyin daloli domin kula da aikin fadada wannan masallacin da kuma tsaftace shi.

You may also like

Leave a Comment

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More