HARIN MAKAMIN ROKET

by Datti

SUBHANALLAH

Yau Asabar annoba ‘yan Boko Haram ISWAP sun kaddamar da harin makamai masu linzami a unguwar gida dubu da kuma yankin Ngomari dake kusa da filin jirgin saman Maiduguri inda suka harba makaman roket, zuwa yanzu ba’a san adadin barnan da sukayi ba

Duk mai bincike akan ayyukan ta’addanci da suke faruwa a Arewacin Nigeria, idan ya tsaya ya duba da kyau zai fahimci akwai wasu manyan azzalumai maciya amanar tsaro wadanda basa so a kawo karshen ta’addancin a Arewa, sai abin ya lafa bayan kwana biyu sai su dawo dashi don kar hanyoyin samun kudi su yanke

Shugabannin da muke da su ‘yan siyasa ba damuwarsu bane halin barazana da talakawa suke ciki, suna da karfin ikon da zasu iya dakatar da wannan rashin hankali na ‘yan ta’adda amma ba zasuyi ba saboda ba su ake cutarwa ba

Muna fatan Allah Ya kawo mana karshen duk wani azzalumi maciyin amanar Arewa

Arewa Intelligence
4-12-2021

You may also like

Leave a Comment

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More